RUNDUNAR SOJOJIN ƘASAN NAJERIYA TA YI TIR DA ƊABI’AR WATA HAFSA.
Rundunar sojojin ƙasan Najeriya ta yi Allah wadai da halin wata hafsa wadda ta ci zarafin wata ƴar bautan ƙasa a Calabar da ke jihar Cross River. Cin zarafin ya na ƙunshe ne a cikin wani bidiyo wanda ke yawo a yanar gizo.
Rundunar sojin ƙasan a matsayin ta na abin alfaharin Najeriya da kuma jagorar haɗin kai na girmama ƴancin ɗan Adam ne ta yi Allah wadai da mummunar ɗabi’ar ƙaramar hafsar wanda ya kunƴata rundunar a idon duniya.
Wannan al’amari dai ya faru ne a Birged
na 13 da ke garin Calabar na jihar Cross River. Tuni dai Kwamandan rundunar ya kafa kwamitin bincike na musamman da kuma ɗaukar matakin da ya dace akan hafsar kamar yadda kudin dokokin dakarun soji ta tanada.
Haka kuma zargin da ake yi cewa Birged na 13 na niyyar lulluɓe maganar ƙariya ce tsagoranta. Rundunar na tabbatar wa al’umma cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen magance wannan al’amari. Ta na kuma ƙara tabbatar ma su cewa za ta kare ƴancin ɗan adam kamar yadda doka ta tanada.
Saboda haka ne ma rundunar ta samar da sashen kula da ƴancin ƴan adam a duk rundunanonin sojin ƙasan. Rundunar sojin ta na ba da haƙuri akan wannan al’amari musamman ga ƴar yi ma ƙasa hidimar, abokan ta, dangin ta, da ma hukumar kula da masu yi ma ƙasa hidima da dukkan al’umma bi sa wannan al’amarin da ya gabata.
BIRGEDIYA JANAR ONYEMA NWACHUKWU
DARAKTAN HULƊA DA JAMA’A NA RUNDUNAR SOJOJIN ƘASAN NAJERIYA
23 SATUMBA 2021